Wednesday, March 11
Shadow

Kowane Musulmi Imaninsa Yana Cika Ne Idan Ya Yarda Tare Da Rungumar Kowace Irin Kaddara Ce Ta Same Shi, Cewar Sarki Sanusi II A Hudubarsa Ta Yau Juma’a

Kano
Daukar ƙaddara mai kyau ko mara kyau yana daga cikin cikar imanin mutum -inji Sarki Sanusi a huɗubarsa ta yau Juma'a Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya ce babu wanda zai iya tuhumar Allah dangane da ƙaddara. Sabon sarkin ya faɗi hakan ne yayin huɗubar sallar Juma'a a masallacin sarki da ke Ƙofar Kudu a birnin Kano. Huɗubar dai ta mayar da hankali ne kan imani da ƙaddara mai kyau ko marar kyau. " Duk wanda ya yi imani da Allah shi kaɗai to dole ne ya yi imanin duk abin da Allah ya ƙaddara. Ba a tambayar ubangiji dalilin aiwatar da al'amura. An faɗa mana cewa duk wanda bai yarda da ƙaddara ba cewa daga Allah take, imaninsa bai cika ba. Ya kamata mu zama masu godiya ga Allah a yanayi daɗi ko wuya. Dole ne mu yarda cewa duk abin da ya faru a gare mu ta ƙaddara ce daga Allah,...
Hoto:An kamashi Saboda sayar da ‘ya’yanshi har guda 6 a jihar Sokoto

Hoto:An kamashi Saboda sayar da ‘ya’yanshi har guda 6 a jihar Sokoto

Duk Labarai
'Yansanda a jihar sokoto sun kama wani mutum saboda siyar da 'ya'yansa 6. Mutumin ya sayar da jimullar kananan yara 28 ciki hadda 'ya'yan cikinsa 6. Kwamishinan 'yansandan jihar, CP Ali Hayatu Kaigama ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace an kubutar da 21 daga cikin yaran. Mutumin me suna, Bala Abubakar yana baiwa wasu mata, Kulu Dogon yaro da Elizabeth Ojah yaranne inda su kuma suke bashi Naira dubu dari da hamsin ko kuma Naira dubu dari biyu da hamsin. Ana cewa wai za'a kaisu Abujane wajan wani mutum da zai rika kula dasu.
Kalli Hotuna: An kamashi da ma-ka-mai wanda yake shirin sayarwa da ‘yan Bindiga

Kalli Hotuna: An kamashi da ma-ka-mai wanda yake shirin sayarwa da ‘yan Bindiga

Tsaro
'Yansanda a jihar Filato sun kama wani mutum me matsakaitan shekaru da makamai da yake shirin kaiwa 'yan Bindiga. Mutumin ya taho ne daga jihar Zamfara. An kama mutuminne a tashar mota ta NTA park dake Jos. Shugaban tashar, Ibrahim Maikwudi ya tabbatarwa da manema labarai da faruwar lamarin. Yace kadan ya rage mutane su kashe wanda ake zargin amma jami'an tsaro suka tseratar dashi.
A cikin shekara daya da muka yi muna mulki, mun yi maganin Boko Haram>>Gwamnatin Tinubu

A cikin shekara daya da muka yi muna mulki, mun yi maganin Boko Haram>>Gwamnatin Tinubu

Tsaro
Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta bayyana cewa ta yi nasarar yin maganin kungiyar Boko Haram. Gwamnatin ta bayyana hakane ta bakin sakataren gwamnatin tarayyar, George Akume. Ya bayyana hakane a Abuja wajan kaddamar da wani Littafi da aka yi kan cika shekara daya da kafuwar Gwamnatin Tinubu. Yace babu wanda zai yi jayayyar cewa gwamnatin Bola Ahmad Tinubu ta yi nasarar gamawa da Kungiyar Boko Haram. Saidai yace har yanzu suna yaki da Kungiyar masu garkuwa da mutane.
An kama mahaifi dan Najeriya saboda zane diyarsa

An kama mahaifi dan Najeriya saboda zane diyarsa

Duk Labarai
'Yansanda a jihar Legas sun kama wani mahaifi me suna Olamide Fatumbi me kimanin shekaru 25 saboda dukan diyarsa me shekaru 3. Mutumin na zaunene a Afeez Street, Akesan, Igando, Lagos State kuma an zargeshi da cutarwa ga diyar tasa. Saidai ya musanta zarge-zargen da akw masa. Mai Shari'a, Mrs E. Kubeinjeya bayar da belin wanda akw zargi akan Naira dubu dari(100,000) da kuma mutane 2 da zasu tsaya masa. An dage sauraren karar sai nan da zuwa 25 ga watan Yuni.
Hoto: An kama Wani mutum da yayi yunkurin sayar da diyarsa me shekaru 5 akan Naira Miliyan 1.5 a jihar Bauchi

Hoto: An kama Wani mutum da yayi yunkurin sayar da diyarsa me shekaru 5 akan Naira Miliyan 1.5 a jihar Bauchi

Bauchi
Ƴan sanda sun cafke wani mutum a Bauchi da ya yi yunkurin sayar da ‘yarsa Naira milyan ɗaya da rabi (N1.5m) Magidancin dan shekara 39 mai suna Yusuf Umar da ke kauyen Dagu a karamar hukumar Warji a jihar Bauchi yayi yunkurin $ayar da diyarsa mai shekaru 5 a kan kudi naira miliyan 1.5 bayan sun rabu da mahaifiyar yarinyar, Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Auwal Musa Mohammed ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai tare da gabatar da wanda ake zargin a hedikwatar ‘yan sandan da ke Bauchi.
Zamu rama kashe mana sojoji 5 da kungiyar IPOB suka yi, zamu tabbatar mun yi maganinsu>>Inji Hukumar sojojin Najeriya

Zamu rama kashe mana sojoji 5 da kungiyar IPOB suka yi, zamu tabbatar mun yi maganinsu>>Inji Hukumar sojojin Najeriya

Tsaro
Hukumar sojojin Najeriya ta tabbatar da kisan sojoji 5 da kungiyar IPOB suka yi. Hukumar tace an kashe sojojin ne dake rundunar Operation UDO KA da aka kai Obikabia. Tace akwai kuma farar hula 6 da suma aka kashe a yayin harin. Kakakin hedikwatar tsaro, Majo Janar Edward ne ya bayyana hakan inda yace zasu tabbatar sun rama wannan kisan da aka musu. Hukumar sojin tace maharan sun je wajanne a motocin Prado 3 dake da bakin gilashi sannan akwai wasu kuma a yankin da suma suka farwa sojojin.