Friday, December 19
Shadow
Da Duminsa: Akwai yiyuwar Najeriya zata iya kaiwa ga gasar cin kofin Duniya na 2026 duk da Dr. Congo ta cireta

Da Duminsa: Akwai yiyuwar Najeriya zata iya kaiwa ga gasar cin kofin Duniya na 2026 duk da Dr. Congo ta cireta

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, har yanzu akwai yiyuwar Najeriya ta samu damar buga gasar cin kofin Duniya na shekarar 2026 wanda za'a yi a kasashen Amurka, Canada, da Mexico. Hakan na zuwane bayan da hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF ta shigar da korafi a gaban hukumar kwallon kafa ta Duniya, FIFA inda take cewa wasu daga cikin 'yan wasan kasar Dr. Congo basu cancanci yi wa kasar wasa ba. Korafin na cewa akalla 6 zuwa 9 na 'yan wasan Dr. Congo sun koma 'yan kasar ta Dr. Congo ne daga wasu kasashe daban-daban kuma ma har FIFA ta tantancesu ta amince da hakan. Saidai NFF sun gano cewa, daga cikinsu akwai wadanda basu bar kasashen su na baya ba, watau ma'ana suna rike da fasfon kasashe biyu, wanda kundin tsarin mulkin kasar Dr. Congo ya haramta rike fasfon kasashe Biyu. Yanzu dai...
Kalli Bidiyon irin abinda matasa sukawa gidan mutumin da yayi aika-aika a masallacin Hotoro dake Kano

Kalli Bidiyon irin abinda matasa sukawa gidan mutumin da yayi aika-aika a masallacin Hotoro dake Kano

Duk Labarai
Bayan Kàshè mutumin da ya yànqà ladani ya ciro maqogoronsa a masallaci a Hotoro Kano, matasan unguwar sun kuma je gidan wanda yayi aika aikar suka cinna masa wuta. Wannan Bidiyon yanda lamarin ya kasancene inda mutane suka taru suna mayar da zantuka. https://www.tiktok.com/@ibrahim.general/video/7584394566707481864?_t=ZS-92GvQoakyIq&_r=1 https://www.tiktok.com/@young.journalist69/video/7584204856735304971?_t=ZS-92GvtL9hlEP&_r=1
Ba zan kara yin wani aure ba>>Inji A’isha Buhari

Ba zan kara yin wani aure ba>>Inji A’isha Buhari

Duk Labarai
Matar marigayi tsohon shugaban kasa, Hajiya A'isha Buhari ta bayyana cewa, ba zata sake yin wani aure ba. Hajiya A'isha ta bayyana hakane a littafin da aka rubuta na rayuwar tsohon mijinta, kuma tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari. Tace miji daya ya isheta. Sannan kuma tace zata ci gaba da rayuwa a tsakanin 'ya'yanta da Jikoki da abokai. Tace zata ci gaba da kula da gidauniyarta.
Da Duminsa: Shugaba Tinubu ya fasa karawa Dogarinsa girma zuwa Brigadier General bayan da wasu tsaffin sojoji suka shiga maganar

Da Duminsa: Shugaba Tinubu ya fasa karawa Dogarinsa girma zuwa Brigadier General bayan da wasu tsaffin sojoji suka shiga maganar

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya fasa karawa Dogarinsa, Yusuf Nurudeen girma daga mukamin Colonel zuwa Brigadier General. A watan Janairu da ya gabata ne dai aka kara masa girma zuwa Colonel. Inda a yanzu kuma ake son kara masa girma zuwa Brigadier General. Amma a doka sai ya shekara 4 yana mukamin Colonel kamin ya je yayi wata horaswa sannan a kara masa mukamin zuwa Brigadier General. Saidai Shugaba Tinubu ya so ya masa karin girman ba tare da bin waccan matakai ba. Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, wasu tsaffin janarorin sojane suka shiga maganar shiyasa aka fasa karin mukamin da aka shirya yi ranar Litinin.
Da Duminsa: Kakakin Majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio ya halarci zaman majalisar na yau yayin da ake rade-radin cewa ya yanke Jiki ya Fhàdì an garzaya dashi Asibiti

Da Duminsa: Kakakin Majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio ya halarci zaman majalisar na yau yayin da ake rade-radin cewa ya yanke Jiki ya Fhàdì an garzaya dashi Asibiti

Duk Labarai
Rahotanni daga majalisar Dattijai sun tabbatar da cewa, kakakin majalisar, Godswill Akpabio ya halarci zaman majalisar na yau. Hakan na zuwane bayan da rahotanni suka watsu cewa ya yanke jiki ya fadi an garzaya dashi asibitin kasar Landan. Akpabio ya koka da matsalar watsuwar labaran karya inda yace suna da wahalar magancewa. Majalisar dai ta nemi hukumar ofishin me baiwa shugaban kasa shawara akan harkar tsaro, NSA su binciki yanda aka yi labarin ya yadu.
Kalli Bidiyon: A karin Farko an hango Jirgin saman sojojin Najeriya, C-130 dake ajiye a filin jirgin kasar Burkina Faso

Kalli Bidiyon: A karin Farko an hango Jirgin saman sojojin Najeriya, C-130 dake ajiye a filin jirgin kasar Burkina Faso

Duk Labarai
An Hango jirgin saman sojojin Najeriya C-130 dake ajiye a filin jiragen saman kasar Burkina Faso. Jirgin dai na dauke da sojoji 11 ne na Najeriya da hukumomin Najeriya suka ce ya samu tangarda a hanyarsa ta zuwa kasar Portugal ya sauka a kasar ta Burkina Faso. Saidai hukumomin kasar Burkina Faso sun zargi akwai wata maqarqashiya game da saukar jirgin a kasarsu. https://twitter.com/GallantDaletian/status/2000892186674528536?t=yxeUTLLX9UFobJ9bdyftuw&s=19
Ji yanda na kusa da Buhari suka so a tsayar da Sanata Ahmad Lawal takarar shugaban kasa a APC

Ji yanda na kusa da Buhari suka so a tsayar da Sanata Ahmad Lawal takarar shugaban kasa a APC

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, na kusa da Marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari sun yi kokarin ganin an tsayar da Sanata Ahmad Lawal takarar shugaban kasa a jam'iyyar ba Tinubu ba. Rahoton yace wadannan mutane sun rubuta takardar Boge inda suka ce daga shugaban kasa ne suka mikawa shugaban 'yansanda da shugaban DSS suka basu Umarnin su tabbatar Sanata Sanata Ahmad Lawal ne ya zama dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC. Saidai shugaban 'yansandan a wancan lokacin ya nemi tabbatar da wannan umarni kai tsaye daga wajan shugaba Buhari inda Buharin yace ba gaskiya bane. Hakan ya bayyana ne a sabon Littafin da aka rubuta da ya kunshi tarihin rayuwar tsohon shugaban kasar wanda aka kaddamar a fadar shugaban kasa jiya.