Friday, December 19
Shadow
Kalli Bidiyon: Darikar Tijjaniyya Khafurci ne kuma Wallahi ko dana ya shigeta sai na tsyne mai Albarka na koreshi daga gidana>>Inji Wannan malamin

Kalli Bidiyon: Darikar Tijjaniyya Khafurci ne kuma Wallahi ko dana ya shigeta sai na tsyne mai Albarka na koreshi daga gidana>>Inji Wannan malamin

Duk Labarai
Malamin Addinin Islama ya bayyan cewa Darikar Tijjaniyya Kafurcice. Malam ya bayyana hakane a wani Bidiyonsa da yake wa'azi inda yace ko mahaifinsa ne ya shiga Darikar Tijjaniyya to ya kafurta Hakanan yace ko dansa ya shiga Darikar Tijjaniyya sai ya tsine masa ya koreshi daga gidansa https://www.tiktok.com/@ibn.ali.alzakzaky/video/7570007527878937876?_t=ZS-91DCXAE1tgm&_r=1
Da Duminsa: Kasar Rasha ma ta yi magana kan Bharazanar Kharin da Trump yace zai kawo Najeriya

Da Duminsa: Kasar Rasha ma ta yi magana kan Bharazanar Kharin da Trump yace zai kawo Najeriya

Duk Labarai
Kasar Rasha a karin farko ta yi magana akan Barazanar harin da shugaban kasar Amurka, Donald Trump yace zai kawo Najeriya. Kasar ta bakin me magana da yawun ma'aikatar harkokin kasashen waje, Maria Zakharova tace tana saka ido akan Najeriya da abinda ka iya faruwa Ta yi kira ga kowane bangare dasu mutunta dokokin kasa da kasa. Hakan na zuwa ne bayan da kasar China tace tana tare da Najeriya sannan bata goyon bayan kowace kasa ta kawowa Najeriya Khari.
Kalli Bidiyo: Hadiza Gabon baki kyauta kin ba, Na yi Hira dake kin je kin yi Editing ana ta Zhagina>>Inji Tauraron fina-finan Hausa, Musbahu Anfara

Kalli Bidiyo: Hadiza Gabon baki kyauta kin ba, Na yi Hira dake kin je kin yi Editing ana ta Zhagina>>Inji Tauraron fina-finan Hausa, Musbahu Anfara

Duk Labarai
Tauraron fina-finan Hausa, Musbahu Anfara ya bayyana rashin jin dadinsa kan yanda Hadiza Gabon ta yi Editing hirar da yayi da ita a shirin ta na Gabon Show. Ya bayyana cewa bai ji dadin hakan ba. Hakanan ya baiwa shuwagabannin gidan Solo Hakuri kan kalaman da yayi. Saidai yace masu zaginsa su ci gaba dan yanzu a kafafen sada zumunta kowa ma zagi ake. https://www.tiktok.com/@misbahu.aka.anfara/video/7569954858669821191?_t=ZS-91D8HvUZCOe&_r=1
Kundin Tarihin Duniya ya baiwa ‘Yar Najeriya, Hilda Baci shaidar shiga tarihin Duniya bayan data dafa shinkafa Dafaduka a Tukunya mafi girma a Duniya

Kundin Tarihin Duniya ya baiwa ‘Yar Najeriya, Hilda Baci shaidar shiga tarihin Duniya bayan data dafa shinkafa Dafaduka a Tukunya mafi girma a Duniya

Duk Labarai
Kundin bajinta na 'Guinness World Records' ya karrama matashiyar nan yar Najeriya Hilda Baci saboda girka dafa-dukar shinkafa mafi yawa a duniya. A watan Satumban da ya gabata ne matashiyar ta yi wani gagarumin aikin girka dafa-dukar shinkafa mafi yawa cikin tukunya ɗaya a duniya. Dafa-dukar shinkafa da ake yi wa laƙabi da 'jollof' abinci ne da ya shahara a ƙasashen Najeriya da Ghana da Senegal da Saliyo da Laberiya da ma wasu da dama. Hilda mai shekara 28 a duniya ta yi shuhura ne a shekara ta 2023 bayan kafa tarihin kwashe lokaci mafi tsawo tana girki ita kaɗai, na tsawon sa'a 93 da minti 11
Shugaban kasa, Tinubu ya gana da sarkin Musulmi

Shugaban kasa, Tinubu ya gana da sarkin Musulmi

Duk Labarai
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya gana da Sarkin Musulmi Sa'ad Abubaka III a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja yayin da barazanar Trump ta kai hari ƙasar ke ci gaba da jan hankali. Ganawar tasu na zuwa ne bayan Tinubu ya gana da Archbishop na Abuja Ignatius Kaigama. Fadar shugaban ba ta bayyana abin da suka tattauna ba, amma ana sa ran ba za ta wuce yunƙurin kwantar da hankali ba yayin da wasu ke yaɗa iƙirarin yi wa mabiya addinin Kirista kisan ƙare-dangi. Daga baya sarkin ya bi sawun shugaban ƙasar wajen yin sallar Juma'a a fadar shugaban ƙasa
Dole Trump ya fito ya janye kalamansa sannan ya baiwa Najeriya hakuri>>Inji Sanata Barau

Dole Trump ya fito ya janye kalamansa sannan ya baiwa Najeriya hakuri>>Inji Sanata Barau

Duk Labarai
Sanata Barau Jibrin ya bayyana cewa, dolene Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya janye kalaman barazanar da yawa Najeriya sannan ya bayar da hakuri. Ya bayyana hakane a wajan wani taron ganawa da matasa da yayi ranar Alhamis. Sanata Barau yace Najeriya kasa ce me cin gashin kanta dan haka ba zata bari wata kasa ta zo tana mata barazana ko katsalandan ba. Yace ko da abinda Trump yake fada gaskiyane ba sigar da ya kamata ya biyo ba kenan, kamata yayi majalisar Dinkin Duniya ce zata shiga tsakani saboda akwai dokar kasa da kasa. yace mu ba dabbobi bane akwai dokokin da suka tanadi hanyoyin da ake bi dan daukar mataki akan matsaloli irin wannan ba wai barazana ba.
Kalli Bidiyon: Najeriya ce kadai kasar Duniya da aka ce za’a kawowa Khari amma aka mayar da Abin Comedy>>Inji Malam Aminu Ibrahim Daurawa

Kalli Bidiyon: Najeriya ce kadai kasar Duniya da aka ce za’a kawowa Khari amma aka mayar da Abin Comedy>>Inji Malam Aminu Ibrahim Daurawa

Duk Labarai
Babban malamin Addinin Islama, Malam Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana cewa, Najeriya ce kadai kasar Duniyar da aka ce za'a kawowa Khari amma ta mayar da abin Comedy. Malam na maganane akan harin da kasar Amurka ta yi barazanar kawowa Najeriya. https://www.tiktok.com/@daurawabackup/video/7569761079522233607?_t=ZS-91CGEy8D0SX&_r=1
Ko Gezau: Barzanar Trump bata tsorata mu ba>>Inji Fadar Shugaban kasa

Ko Gezau: Barzanar Trump bata tsorata mu ba>>Inji Fadar Shugaban kasa

Duk Labarai
Fadar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta bayyana cewa, bata kadu da barazanar kawo Khari ta kasar Amurka zuwa Najeriya ba. Ministan yada labarai, Mohammed Idris ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai bayan zaman majalisar zartaswa. Yace shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu bai kadu ba, hakanan Ministocinsa basu kadu ba da barazanar kasar Amirka ta kawo hari ba. Yace saidai tuni suka nema suka fara tattaunawa da wakilan kasar Amurka, yace suna bin hanyar Diplomaciyya dan warware matsalar.
Trump bai isa ya Hana Aiki da shari’ar Musulunci a Jihohin Arewa ba>>Inji Kungiyar Dattawan Arewa

Trump bai isa ya Hana Aiki da shari’ar Musulunci a Jihohin Arewa ba>>Inji Kungiyar Dattawan Arewa

Duk Labarai
Kungiyar Dattawan Arewa, NEF ta mayarwa da shugaban kasar Amirka, Donald Trump da martani me zafi inda tace shugaban Amurkar, Trump bai isa ya hana aiki da Shari'ar Musulunci a Jihohin arewa ba Wasu daga cikin 'yan majalisar kasar Amurka da wasu kungiyoyin fafutuka a kasar sun nuna damuwa kan amfani da shari'ar Musulunci a jihohin Arewa. Dan haka suke kiran a daina amfani da shari'ar Musulunci a Arewa sannan a sakawa wasu jami'an gwamnatin Najeriya takunkumi. Saidai kungiyar NEF ta bakin me magana da yawunta, Prof Abubakar Jiddere tace babu wannan maganar, Trump girman kai ne ke Damunsa kuma barzanar da yake yi ta banza da wofi ce babu abinda zai iya. Sannan kungiyar tace babu maganar yiwa Kiristoci Khisan Kyiyashi a Arewa matsalar tsaro tana shafar kowa da kowane. Hakanan ...