Falalar Kwanaki Goma Na Farkon Watan Zul-Hajji
Falalar Kwanaki Goma Na Farkon Watan Zul-Hajji
… don Allah a yada (sharing) domin amfanar wadanda ba su samu damar zuwa aikin Hajji ba.An karbo Hadisi daga ibn Abbas (R.A) ya ce Annabi (SAW) ya ce: ranar daya ga watan zulhijja ita ce ranar da Allah (SWT) Ya gafarta wa Annabi Adam (A.S). Duk wanda ya azimci wannan rana Allah(SWT) Zai gafarta masa kowane irin zunubi tsakaninsa da Shi..(2) Ranar biyu ga Zulhijja ita ce ranar da Allah (SWT) Ya karbi Addu’ar Annabi Yunus (A.S) Ya fitar da shi daga cikin kifin da ya hadiye shi. Wanda ya azimci wannan rana yana da lada kwatankwacin wanda ya raya shekara da ibada ..(3) Ranar uku ga Zulhijja ita ce ranar da Allah (SWT) Ya karbi addu’ar Annabi Zakariyya (A.S) Ya ba shi haihuwa. Duk wanda ya azimci wannan rana Allah (SWT) Zai karbi adduo’in sa..(4...








