Wannan matar ta dauki hankula bayan da ta yi kiran a samar da Ital din Musulmai Zallah.
Tace ya kamata a samar da Otal na Halal.
https://twitter.com/Teeniiola/status/2005166488895062352?t=xWoBZ58qEXVJTEV72aBQRg&s=19
Wannan wani bayerabene da ya dauki hankula bayan da yace kaf Najeriya kabilar Yarbawa tafi sauran Kabilu daukaka da ci gaba.
Ya bayyana cewa ba a Najeriya kadai ba har ma da kasashen waje akwai Yarbawa wadanda sun daukaka sosai sun zama 'yan majalisa sun rike mukamai sosai a kasashen Amurka da Ingila.
https://twitter.com/Teeniiola/status/2005151519432462345?t=LLZ44fIQY4g9XToR6NBPfg&s=19
Tauraruwar Mawakiya, Tiwa Savage ta sha ruwan Allah wadai saboda kayan data saka a wajan wani wasa da ta yi.
Da yawa sun ce bai kamata ta saka wadannan ayan data saka ba musaman lura da cewa ta haura shekaru 40 kuma ita uwace tana da da.
https://twitter.com/instablog9ja/status/2004880406110498905?t=-Dd6P4KAUpDU0BKuvwMVsA&s=19
Inyamuri da yayi ikirarin yana aiki a matsayin sojan kasar Amurka, ya jawo hankalin 'yan uwansa inyamurai dake zaune a Arewa su koma gida.
Ya bayyana cewa akwai wani abu dake shirin faruwa a Arewacin Najeriya.
Ya bayyana hakane a wani Bidiyosa da ya watsu sosai a kafafen sada zumunta inda da yawa Inyamurai 'yan uwansa suka goyi bayansa.
https://twitter.com/KizyUzoma/status/2004891885916356669?t=HjKJAJbEvj6xqnWI9iFRlw&s=19
A yayin da cece-kuce suka yi yawa akan haska shirin labarina duk da rasuwar daya daga cikin jaruman fim din watau, Fulani, Bangaren Me shirya fim din, Malam Aminu Saura sun yi karin Haske.
Ahmad Nagudu wanda daya ne daga cikin na kusa da Malam Aminu Saira yace ya je jana'izar Fulani ba kamar yanda ake cewa babu wanda ya halarci jana'izar marigayiyar ba.
Yace kuma shirin Labarina tun ranar Laraba aka dorashi.
Yace kuma akwai kamfanoni da suka riga suka bayar da talla
Yace kuma Aminu Saira yayi kokarin a dakatar da fim din ama abu ya gagara.
https://www.tiktok.com/@mjplus_original/video/7588706466115210517?_t=ZS-92akZMzQZxh&_r=1
An ga Tauraron fina-finan Hausa, Tijjani Asase cikin hawaye yana jimamin Rasuwar Tauraruwar jarumar Fim din Labarina, Fulani.
Yayi kira ga abokan aikinsa 'yan Fim da cewa su rika tuna mutuwa su rika kallon wadanda suka rasu sannan su yi hattara da irin abinda suke shukawa.
https://www.tiktok.com/@arewatiktok54/video/7588688334625459463?_t=ZS-92ajLctPnIv&_r=1
Dan kwallon Arsenal, Bukayo Saka ya baiwa wani matashin masoyinsa kyautar takalmin kwallonsa bayan wasansu da Brighton.
An ga Saka ya bashi takalmin a yayin da yake fita daga filin wasan wanda Arsenal ta ci 2-1.
https://twitter.com/DailyAFC/status/2005026639668019322?t=wz8ipSq5HTbCIrMvZKOygw&s=19
Dan wasan Najeriya, Wilfred Ndidi ya ciwa Najeriya kwallonsa ta farko a jiya a wasansu da Tunisia.
Bayan cin kwallon yayi irin murnar cin kwallon da tsohon dan kwallon Najeriya, Kanu Nwankwo ke yi wadda yake dukar da kai yana rawa.
Lamarin ya dauki hankula sosai.
https://twitter.com/ChuksEricE/status/2005054465439924640?t=K3c6l4QmXfeR33U2OwXGcQ&s=19
Tauraruwar mawakiyar Amirka, Nicki Minaj ta rasa mabiya Miliyan 4 a shafinta na Instagram.
Hakan ya faru ne bayan data nuna goyon baya ga shugaban Amirkar, Donald Trump.
Sannan tace tana goyon bayan harin da zai kawo Najeriya.
Yanzh haka dai an kaddamar da kiraye-kirayen a koreta daga Amurka ta koma kasarta, ta Asali watau Trinidad.
A ci gaba da gasar cin kofin Aftika na AFCON, Najeriya ta ci Kasar Tunisia kwallaye 3-2
Najeriya ta sakawa Tunisia kwallaye 3 ta hannun Ndidi, Osimhen da Lookman.
Saidai ana daf da tashi, Tunisia ta farke kwallaye 2 inda a haka aka tashi wasan.
Hakan yasa Najeriya ta tsallake zuwa mataki na gaba.