Farashin da ake sayen dalar Amurka a yau, 20 ga watan October na shekarar 2025 shine Naira ₦1,468–₦1,475 a tsakanin bankuna.
Daga CBN kuma ana sayenta akan Naira, ₦1,467.43 kan kowace dala.
Sai kuma a kasuwar canji ana sayen dalar akan Naira ₦1,480 — Sell ₦1,500
Rahotanni daga babban birnin tarayya, Abuja na cewa, Dan Gwagwarmaya, Omoyele Sowore da sauran masu zanga-zangar neman a saki Nnamdi Kanu sun fito zanga-zangar.
Hakan ya kawo tsaikon ababen hawa sosai a Abujar.
Tuni dai jami'an tsaro suka budewa masu zanga-zangar wuta wanda hakan yasa suka tsere ciki hadda shugaban zanga-zangar, Sowore wanda aka ganshi yana gudu.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Sowore yace 'yansandan sun kama Kanun Nnamdi Kanu da kuma Lauyansa sannan sun lakada musu duka.
Yace suna neman a sake su nan take.
https://twitter.com/YeleSowore/status/1980167258308841500?t=nkVhQT-0xbwX_Zee6L7W7Q&s=19
https://twitter.com/ArcSadam/status/1980172085583655235?t=576w70RrqZt4fHM2bAxnRg&s=19
Sanata Orji Uzor Kalu na neman a mayar da mulkin Najeriya na tsawon shekaru 6 amma wa'adi daya ga shugaban kasa da Gwamnoni.
Ya jawo hankalin sanatoci 'yan uwansa dasu dauki wannan matsaya inda yace hakan zai baiwa shugaban kasa da Gwamnoni damar tsayawa su gudanar da mulki ba tare da neman zarcewa ya rika dauke musu hankali ba.
Ya bayyana hakane a cikin wani Bidiyosa daya watsu sosai a kafafen sada zumunta.
https://twitter.com/NigeriaStories/status/1979971959090754026?t=Il_qxj0sVMj9CePn3WI-yA&s=19
Ministan kudi, Wale Edun ya dawo gida Najeriya bayan jinyar da yayi a kasar Ingila.
Wale Edun ya dawo Najeriya ne tare da tawagarsa.
A baya dai an yada cewa Ministan ya kwanta rashin lafiya inda cutar shanyewar rabin jiki ta kamashi.
Saidai daga baya Gwamnati ta musanta cewa ba cutar shanyewar rabin jiki bace ta kamashi amma dai da gaske bashi da lafiya.
Rahotanni sun bayyana cewa, Wani tsohon Gwamnane daga kudancin Najeriya ake zargi da hannu a shiryawa yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu juyin Mulki.
Rahotanni sun ce ana zargin Tsohon Gwamnan ne ya samar da kudaden da za'a gudanar da juyin mulkin kamar yanda gidan jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Rahoton yace har yanzu ana binciken alakar dakar tsakanin tsohon Gwamnan da sojojin da suka shirya juyin mulkin, kuma da zarar an samu tabbacin hannunsa, za'a gayyaceshi dan amsa tambayoyi.
Rahoton yace ana kiyaye sunayen sojojin da suka shirya juyin mulkin dan kada a fitar dasu amma Daily Trust tace ta samu cewa akwai soja Brigadier general da kuma Captain.
Tace kuma ana sojojin daya ya fito daga jihar Naija ne yayin da dayan ya fito daga jihar Nasarawa kuma yana da alaka da gida...
Malam ya bayyana cewa sau 3 yana mafarki da Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam).
Yace 'yan Bidi'a karya suke ba masoya Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) bane na gaskiya.
Yace 'yan Bidi'a su zo a basu kalmar shahada.
https://www.tiktok.com/@ali_d_abba/video/7561175476643826966?_t=ZS-90hTc6ehUfp&_r=1
Rahotanni sun bayyana cewa, masu shirya zanga-zangar neman a saki shugaban Haramtacciyar kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu a yau Litinin, Sun ce ba gudu ba ja da baya duk da gargadin da jami'an tsaro suka musu.
Masu zanga-zangar sun shirya yin tattaki zuwa fadar shugaban kasa dan neman a saki Nnamdi Kanu.
Hakan kuma na zuwane a yayin da Babbar kotun gwamnatin tarayya ta hana masu zanga-zangar zuwa kusa da fadar gwamnati ko kuma kuma majalisar tarayya ko duk wani ginin gwamnati.
Saidai duk da wannan, masu zanga-zangar sun ce ba gudu ba ja da baya, hakanan shugaban Zanga-zangar, Omoyele Sowore yace maganar umarnin Kotun ba gaskiya bane.
Idan dai masu zanga-zangar suka fito, akwai yiyuwar za'a yi dauki ba dadi tsakaninsu da jami'an tsaro.
Malamin Addinin Islama, Sheikh Sani Yahya Jingir ya bayyana cewa, Ba zai daina son Tikitin takarar shugaban kasa na Muslim Muslim ba.
Yace ba dan kowa yake yi ba sai don Allah.
Malam yace bai hana kowa yin nashi ba amma kuma shima babu wanda zai hanashi yin nashi.
https://www.tiktok.com/@i_am_saeed01/video/7562482931617336588?_t=ZS-90gKuhqfIoK&_r=1
Wani dan Dariqa da ake kira da Abu Hanifa ya bayyana cewa ya bar Dariqar.
Yace ya bar Shirka da Kafirci inda yace ba dama mutum ya ga ba daidai ba yayi magana sai a rika kiransa da munafiki.
Ya bayyana hakane a wani Bidiyonsa da ya wallafa a shafinsa na Tik.
https://www.tiktok.com/@sanusi.umar18/video/7562128044677287169?_t=ZS-90g75j8pRZY&_r=1
iGwamnatin jihar Kano ta rufe wajan shan shisha me suna Arfat Shisha Lounge
Hukumar kula da yawon shakatawa ta jihar hadi da hukumar yaki da shan miyagun kwayoyi, NDLEA ne suka rufe wajan shan shishar.
Shugaban hukumar shakatawar Alhaji Tukur Bala Sagagi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa inda yace wannan kokari ne na kawar da ayyukan ta'ammuli da miyagun kwayoyi a jihar.
Yace a jihar ta Kano, Akwai dokar Haramta shan Shisha kuma zasu ci gaba da karfafa wannan doka.