Saturday, December 6
Shadow
Kalli Bidiyo: Na bar Shirka da Kafurcin Dariqa, daga yau na fita daga Dariqa>>Inji Abu Hanifa

Kalli Bidiyo: Na bar Shirka da Kafurcin Dariqa, daga yau na fita daga Dariqa>>Inji Abu Hanifa

Duk Labarai
Wani dan Dariqa da ake kira da Abu Hanifa ya bayyana cewa ya bar Dariqar. Yace ya bar Shirka da Kafirci inda yace ba dama mutum ya ga ba daidai ba yayi magana sai a rika kiransa da munafiki. Ya bayyana hakane a wani Bidiyonsa da ya wallafa a shafinsa na Tik. https://www.tiktok.com/@sanusi.umar18/video/7562128044677287169?_t=ZS-90g75j8pRZY&_r=1
Gwamnatin Kano ta rufe wajan shan Shyshaa me suna ARAFAT

Gwamnatin Kano ta rufe wajan shan Shyshaa me suna ARAFAT

Duk Labarai
iGwamnatin jihar Kano ta rufe wajan shan shisha me suna Arfat Shisha Lounge Hukumar kula da yawon shakatawa ta jihar hadi da hukumar yaki da shan miyagun kwayoyi, NDLEA ne suka rufe wajan shan shishar. Shugaban hukumar shakatawar Alhaji Tukur Bala Sagagi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa inda yace wannan kokari ne na kawar da ayyukan ta'ammuli da miyagun kwayoyi a jihar. Yace a jihar ta Kano, Akwai dokar Haramta shan Shisha kuma zasu ci gaba da karfafa wannan doka.
Wani Magidanci ya je ofishin ‘yansanda na jihar Kano inda yace zai kara aurene shine ya baiwa matarsa Naira Miliyan 2 toshiyar baki, shine yake neman shawara ko hakan ya sabawa doka?

Wani Magidanci ya je ofishin ‘yansanda na jihar Kano inda yace zai kara aurene shine ya baiwa matarsa Naira Miliyan 2 toshiyar baki, shine yake neman shawara ko hakan ya sabawa doka?

Duk Labarai
Wani magidanci ya je ofishin 'yansanda na jihar Kano inda yace zai kara aurene dan haka ya baiwa matarsa toshiyar baki ta Naira Miliyan 2. Shine yake neman shawara ko hakan ya dace da doka? Kakakin 'yansandan jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya wallafa labarin a shafinsa na Facebook.
Kalli Bidiyon yanda aka shirya yakin neman zabe a Legas dan kira ga Shugaba Tinubu ya fito takara a 2027

Kalli Bidiyon yanda aka shirya yakin neman zabe a Legas dan kira ga Shugaba Tinubu ya fito takara a 2027

Duk Labarai
Mutane da yawa ne a Legas suka fito dan kira ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya sake fitowa takara a shekarar 2027. An ga mutanen na daga kwalaye masu dauke da hotunan shugaban kasar. Saidai wasu sun yi zargin an baiwa mutanen kudi ne. Hakanan hukumar zabe me zaman kanta INEC a hana irin wannan yakin neman zabe tun kamin lokacin zabe yayi. https://twitter.com/GossipMillNaija/status/1979661716872216952?t=7guCszb453jpOzWzCHCLGg&s=19
Babban Sojan Najeriya Lt. Col. Aliyu Saidu Paiko da wasu sojoji 5 dake tare dashi sun rigamu gidan gaskiya a fagen daga a jihar Borno

Babban Sojan Najeriya Lt. Col. Aliyu Saidu Paiko da wasu sojoji 5 dake tare dashi sun rigamu gidan gaskiya a fagen daga a jihar Borno

Duk Labarai
Sojan Najeriya, Lt. Col. Aliyu Saidu Paiko da wasu sojoji 5 sun rigamu gidan gaskiya a jihar Borno a yayin da aka kai musu Harin Kwantan Bauna. Lamarin ya farune ranar 17 ga watan October 2025 inda kuma aka kashe CJTF 3. https://twitter.com/Edrees4P/status/1979681137967690102?t=BsJtahuOK0wLPAnT2ZDUVA&s=19
Muma Mun samu bayanan cewa lallai an shirya yiwa Shugaba Tinubu Juyin Mulki, kuma Sojojin da aka kama dalilin haka suna da yawa>>Inji Jaridar Punchng

Muma Mun samu bayanan cewa lallai an shirya yiwa Shugaba Tinubu Juyin Mulki, kuma Sojojin da aka kama dalilin haka suna da yawa>>Inji Jaridar Punchng

Duk Labarai
Jaridar Punchng ta zama ta uku kenan data ruwaito cewa, an kama wasu sojoji da suka shirya yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu juyin Mulki. Jaridar tace wata majiyar soji ta tabbatar mata da cewa kamen da kawa wasu sojoji sama da 16 na da alaka da shirin juyin Mulkin da suke shirin yiwa Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. Jaridar Punchng ta kara da cewa wani janar ne ka jagoranar sojojin da ke shirin kifar da Gwamnatin Shugaba Tinubu wanda suka shirya yi ranar 1 ga watan October. Saidai Hukumar sojojin Najeriya ta ce karyane babu wani shirin jurin mulki aka yiwa shugaba Tinubu. Jaridar Sahara reporters ce ta fara kawo labarin tace an kama sojoji 16 inda daga baya Premium times itama ta ce ta samu wanan rahoto inda tace an kama sojoji 20. Rahoton jaridar Punchng yace amma k...
Mutum Biyu sun taba nunawa mamana Bidiyon wakokin da nake yi, na duresu, saboda me yasa zasu nuna mata salon su tayar mata da hawan jini? Inji Soja Boy me waka yana tabawa da Rhunghumar mata

Tauraron mawakin Batsa da kuma waka tare da runguma da taba mata na Arewa, Soja Boy ya bayyana cewa, ya taba daure wasu mutane 2 da suka nunawa mahaifiyarsa Bidiyon wakar da yake. Yace Ai ta zaginshi da tsinuwa bai damu ba amma me zai saka a rika nunawa mahaifiyarsa irin Bidiyon wakokin da ake yi? https://www.tiktok.com/@_soulja.boy/video/7562676307440438549?_t=ZS-90fmkGFdxzd&_r=1
Kalli Bidiyon: Na fara Bushara kuma nan gaba kadan Karfin wa’azina zai sa a Rushe Masallatan Maiduguri>>Inji Abubakar da ya yi ridda koma Kirista

Kalli Bidiyon: Na fara Bushara kuma nan gaba kadan Karfin wa’azina zai sa a Rushe Masallatan Maiduguri>>Inji Abubakar da ya yi ridda koma Kirista

Duk Labarai
Matashi daga jihar Borno da ya yi ridda ya koma Kirista ya bayyana cewa, ya fara Bushara. Yace nan gaba za'a rushe masallatan Maiduguri. Sannan yace ya nemi a bashi aya da tace ayi Sallah sau biyar a Qur'ani amma an kasa dan haka yanzu abinda yake so shine a kawo mai mutum daya daya shiga Aljannah sanadin Qur'ani. https://www.tiktok.com/@musa.n.ndirmbitah/video/7562693046136016136?_t=ZS-90floVSlv2v&_r=1