Wednesday, December 17
Shadow
Dr. Ahmad Gumi ya bukaci gwamnatin Tinubu ta nemi Trump ya janye barazanar da yawa Najeriya idan kuma yaki janyewa Najeriya ta yanke alakar jakadanci da Amurka

Dr. Ahmad Gumi ya bukaci gwamnatin Tinubu ta nemi Trump ya janye barazanar da yawa Najeriya idan kuma yaki janyewa Najeriya ta yanke alakar jakadanci da Amurka

Duk Labarai
Babban malamin addinin Islama, Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya bukaci Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta nemi shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya janye barazanar da yawa Najeriya. Yace shugaba Tinubu ya kira jakadan Amurka ya bukaci kasardu ta janye barazanar da tawa Najeriya. Sheikh Gumi yace kasa bata fi kasa ba, Najeriya kasa ce me con gashin kanta dan haka bai kamata ta tsaya ana gaya mata abubuwan da basu kamata ba. Sheikh Gumi yace idan Trump yaki janye kalaman nasa, Najeriya ta yanke huldar jakadancin da Amurkar. Ya kuma baiwa Gwamnatin shawarar cewa, ta fara neman wasu abokan huldar kasuwanci da sayen makamai bayan Amirka.
Wasu na zargin matatar man Dangote ce data dauko hanyar Zama babu irinta a Duniya ke tsolewa Thurawa ido shine suke son ganin sun daidaita Najeriya

Wasu na zargin matatar man Dangote ce data dauko hanyar Zama babu irinta a Duniya ke tsolewa Thurawa ido shine suke son ganin sun daidaita Najeriya

Duk Labarai
Tun bayan da Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa ana kashe kiristoci da yawa a Najeriya ne da yawa ke ta sharhi da bayyana abinda suka fahimta game da lamarin. Wasu sun bayyana cewa suna zargin ci gaban da matatar man Dangote ta dauko ne inda nan da wani Lokaci Dangoten yace zata zama ta daya a Duniya wajan yawan tace man Fetur da ganga Miliyan 1.4 a kullun shine ya hana Turawa sakat suke kokarin ganin sun Lalata kasar. A gefe guda kuma wasu na ganin cewa Arzikin da Allah yawa Najeriya ne Turawan ke son zuwa su kwasa. Wasu dai na cewa, zuwan Amurka Najeriya da sunan yakar 'yan ta'adda ba abin Alheri bane musamman lura da irin yanda suka lalata kasashen Libya, Afghanistan, Syria da sauransu.
Ku daina Murna, Trump ba ruwanshi da Kirista ko Musulmi kowa zai dandana kudarsa idan ya kawo khari Najeriya>>Sowore ya gayawa ‘Yan Uwansa Kirista

Ku daina Murna, Trump ba ruwanshi da Kirista ko Musulmi kowa zai dandana kudarsa idan ya kawo khari Najeriya>>Sowore ya gayawa ‘Yan Uwansa Kirista

Duk Labarai
Mawallafin jaridar Sahara reporters kuma dan Gwagwarmaya, Omoyele Sowore ya bayyana cewa, Kiristoci su daina murna saboda Shugaban kasar Amurka, Donald Trump yace zai kawo hari dan Khashye masu yiwa kiristoci Khisan Qare dangi. Sowore yace abin zai shafi kowa ne. Shugaban kasar Amurka Donald Trump yace ba zasu zuba ido suna ganin ana kashe Kiristoci ba, yacw idan Gwamnati bata dauki mataki akan lamarin ba zasu dauki mataki ta hanyar soji.
Da Duminsa: Mun fara shirye-shiryen kai Fharmaki Najeriya>>Inji Sakataren Yhaqi na kasar Amurka

Da Duminsa: Mun fara shirye-shiryen kai Fharmaki Najeriya>>Inji Sakataren Yhaqi na kasar Amurka

Duk Labarai
Sakataren Yaki na kasar Amurka, Pete Hegseth ya bayyana cewa sun fara shirin afkawa masu khashe Kiristoci a Najeriya. Yace muddin ba'a dakile matsalar ba suna nan shigowa su Shekye masu Khashe kiristocin. Ya bayyana hakane a matsayin martanin da shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya basu na cewa su shirya kai hari Najeriya idan Gwamnatin Najeriya bata hana kisan da akewa kiristoci ba.
Kalli Bidiyon: Mu bamu da gata ne, su kuma kirista suna da gata shiyasa maganar har ta kai kunnen Trump yayi magana>>Inji Sheikh Nura Khalid

Kalli Bidiyon: Mu bamu da gata ne, su kuma kirista suna da gata shiyasa maganar har ta kai kunnen Trump yayi magana>>Inji Sheikh Nura Khalid

Duk Labarai
Malamin Addinin Islama, Sheikh Nura Khalid ya bayyana cewa, Kirista na da gata da Jagoranci na gari ne shiyasa suka kai kara aka sauraresu. Yace ku kuma matsalar mu ko an kashe mutane karyatawa muke. Malam yace amma mafita itace ace duka 'yan Najeriya ne ake kashewa babu wata maganar addini kawai a kawo mana dauki. https://www.tiktok.com/@digital_imaam/video/7567884525938806034?_t=ZS-913r5SflRoX&_r=1
Zanje in gana da Trump in warware masa zare da abawa>>Shagaba Tinubu bayan da Trump yayi bharhazanar kawo khari Najeriya

Zanje in gana da Trump in warware masa zare da abawa>>Shagaba Tinubu bayan da Trump yayi bharhazanar kawo khari Najeriya

Duk Labarai
Fadar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta bayyana cewa nan gaba kadan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai gana da shugaban kasar Amurka, Donald Trump. Me baiwa shugaban kasar shawara kan harkar sadarwa, Daniel Bwala ne ya bayyana hakan. Yace a kwai kyakkyawar alaka tsakanin Najeriya da Amurka inda yace a baya Amurkar ta sayarwa Najeriya da makamai Wanda ta yi amfani dasu wajan yakar matsalar tsaro. Hakan na zuwane kwana daya bayan da shugaban Amurkar, Donald Trump yayi barzanar kawo hari Najeriya idan gwamnati bata dauki mataki kan harkar tsaro ba.
Kalli Bidiyo: Na yi kuskure dana ce Kuskurene Halittar Talauci>>Inji Gfresh Al-amin

Kalli Bidiyo: Na yi kuskure dana ce Kuskurene Halittar Talauci>>Inji Gfresh Al-amin

Duk Labarai
Tauraron Tiktok, Gfresh Al-amin ya fito ya bayyana cewa, yayi kuskure a kalaman da yayi cewa halittar Talauci kuskurene. Ya bayyana cewa, yana so ya cene an kirkirarwa Najeriya Talauci da gangan. https://www.tiktok.com/@gfreshfanpage/video/7567900923209583880?_t=ZS-913iASUAwlt&_r=1 Gfresh a baya yayi Bidiyon inda ya fadi cewa halittar Talauci kuskurene a yayin da yake magana akan fadan Baana da A'ishatulhumaira.
Kalli Bidiyo: Bazan iya barin waka in koma makaranta ba saboda, masu digiri da yawa basu da abinda nake dashi irin su waya, mota>>Inji Bilal Villa

Kalli Bidiyo: Bazan iya barin waka in koma makaranta ba saboda, masu digiri da yawa basu da abinda nake dashi irin su waya, mota>>Inji Bilal Villa

Duk Labarai
Mawaki Vilal Billa ya bayyana cewa, ba zai iya barin wasannin barkwanci da yake ba ko kuma waka ya koma makaranta ba. Yace akwai masu digirin da sune ke basu kudi hakanan wayar da yake rikewa da motar da yake hawa, masu digiri da yawa ba su da ita. Saidai yace a yanzu zai iya komawa makaranta saboda ya kawo karfi zai iya rike kansa. https://www.tiktok.com/@cuteboy_backup/video/7567688724436602119?_t=ZS-913fbhsQo1B&_r=1
Qhasar Amurka ta zhargi Sarkin Musulmi da hannu wajan Muzhghunawa Kirista

Qhasar Amurka ta zhargi Sarkin Musulmi da hannu wajan Muzhghunawa Kirista

Duk Labarai
Tsohon Magajin garin Blanco City dake jihar Texas a kasar Amurka, Mike Arnold ya zargi me alfarma sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III da hannu wajan kisan kiyashi da aikata Jihadiy akan Kiristoci. Ya bukaci sarkin da ya fito ya kawo hujja wadda ke nuna cewa bashi da hannu a khiysan da akewa Kiristoci a Arewa. Saidai fadar sarkin ta bayyana cewa wannan zargi ne da bashi da tushe ballantana makama. Sannan tace ba zata ma bayar da amsa ba game da zargin. Sakataren fadar, Alhaji Saidu Maccido, yace Gwamnatin tarayya da Majalisar tarayya sun bayar da amsa kan wannan lamari dan haka hankalin sarki akan karfafa zaman lafiya yake ba irin wadannan maganganun ba.