Ba za mu taɓa yin sulhu da ‘yan bindiga ba – Gwamnan Zamfara
Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawan Dare ya jaddada ƙudurin gwamnatinsa na rashin yin sulhu da 'yan bindiga.
Yayin da yake gabatar da jawabi bayan ya shiga wani tattaki da ƙungiyoyin matasan jihar suka shirya a wani ɓangare na bikin ranar Dimokradiyya, Gwamnan Dauda ya ce zai yi duk abin da ya dace domin maido da jihar kan turbar zaman lafiya.
''Jiharmu na da tarihin zaman lafiya, amma sannu a hankali abubuwa suka fara taɓarɓarewa, sakamakon ayyukan ɓata-gari'', inji gwamnan.
Gwamnan ya ce matsalar tsaro matsala ce da ta shafi kowa da kowa, don haka ya yi kira ga al'ummar jihar su haɗa hannu wajen tabbatar da zaman lafiyar jihar.
"A koyaushe ina faɗa ina maimaitawa bai kamata ka yi sulhu da kasasshe ba, mun ga yadda gwamnatocin da suka gabata suka yi yunƙurin sulhu da 'yan bindig...





