An Daure Wani Mutum A Gidan Yari Sakamakon Samun Sa Da Laifin Karbar Batirin Jirgin Kasa Na Sata
A ranar Alhamis ne wata kotun majistare da ke garin Kafanchan a jihar Kaduna, ta yanke wa wani matashi mai suna Chibuzo Emmanuel, dan shekara 40 da haihuwa, hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari, bisa samunsa da laifin karbar baturan jirgin kasa da silinda na sata.
Hukumar NSCDC, ta gurfanar da Emmanuel tare da Adamu Danbaba mai shekaru 52 da laifin sata da kuma karbar dukiyar sata.
Jami'i mai shigar da kara na NSCDC, Mista Marcus Audu, ya shaida wa kotun cewa hukumar kula da layin dogo ta Najeriya da ke yankin Arewa ta tsakiya, Kafanchan, ta shigar da kara a ofishin hukumar a ranar 13 ga watan Mayu.
Audu ya bayyana cewa Danbaba ma’aikacin layin dogo ne ya saci batir din jirgin kasa guda biyu da silinda mai nauyin kilogiram 12 a ofishin sa ya sayar wa Emmanuel akan kudi N24,000...



