
Rahotanni sun bayyana cewa, Peter Obi ya fice daga jam’iyyar ADC.
Peter Obi ya bayyana hakanne a shafinsa na X.
Yace abinda ya koroshi daga jam’iyyar Labour Party ne ya iske a jam’iyyar ADC shiyasa ya yanke shawarar fita daga cikinta
Yace har yanzu yana girmama Atiku Abubakar da shugaban jam’iyyar, David Mark.
Yace ba wai son neman takarar shugaban kasa ko ta mataimakin shugaban kasa ko ta kakakin majalisa ne yasa ya fice daga ADC ba.
Yace ya ficene domin ganin an gyara Najeriya kowa yana jin dadi babu yunwa babu talauci.