Wednesday, April 8
Shadow

Sanata Natasha ta bayyana gaban Kotu a wajan shari’ar kalubalantar dakatar da ita daga majalisa

Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, wadda ke wakiltar yankin Kogi ta Tsakiya ta isa Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a yau Talata don sauraron karar da aka shigar a kanta.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Mai Shari’a Binta Nyako ta sanya ranar yau talata domin sauraron karar raina kotu da shugaban majalisar dattawa ya shigar kan Akpoti-Uduaghan.

Mai Shari’a Nyako ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar Litinin mai zuwa domin ci gaba da sauraron karar gaba ɗaya.

  • Jaridar Arewa
Karanta Wannan  Ba Mu Yi Da Na Sanin Zabar Tinubu Ba, SabodaTunda Nijeriya Ta Samu 'Ýanci Man Fètur Bai Taba Samuwa Kamar Lokacin Mulkin Tinubu Ba, Inji Shamsu Gwaska

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *