Wednesday, October 9
Shadow

Shugaba Tinubu Ya Tallafawa Ma’aikata Da Ɗalibai Da Gudummawar Motocin Sufuri

Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu ya cika alƙawarin da yayi na ba da kyautar motoci ga ƙungiyoyin ƙwadago da na ɗalibai domin sauƙaƙa musu harkokin sufuri.

An ƙaddamar da ba da motocin yau a fadar shugaba ƙasa, Abuja inda aka miƙa motocin bas-bas guda (64) masu amfani da iskar gas ta (CNG) ga shugabancin ƙungiyoyin.

Idan ba a manta ba, tun bayan cire tallafin man fetur ne dai shugaban ƙasar yayi alƙawarin tallafa wa ma’aikata da ɗalibai da motocin sufuri masu amfani da iskar Gas waɗanda za su rage musu kashe kuɗaɗe wajen zirga-zirgarsu ta yau da kullum.

Karanta Wannan  Kalli Kayatattun hotunan Rahama Sadau data saki

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *