Friday, October 16
Shadow

Ban amince da Dan takarar Gwamna da APC ta zaba ba a jihar Gombe>>Inji Pantami

Sheikh Farfesa Isa Ali Pantami ya bayyana cewa bai yadda da dan takarar da Jam’iyyar APC ta zaba ba a jihar Gombe a matsayin dan takarar Gwamna ba.

Pantami ya bayyana cewa nadi ne aka yi wanda ba’a tuntubi sauran ‘yan takara irinsa ba kamin a yi hakan ba kamar yanda doka ta tanada.

Malam yace dan haka masoyansa kada su tayar da fitina su shiryawa zaben fidda gwani.

Yace ya baiwa lauyoyinsa umarnin shiryawa dan daukar matakin da ya dace.

Karanta Wannan  Yadda Gwamnan Kano, Abba Kabir Ya Jagoranci Duba Lafiyar Yaran Da Aka Sako A Asibiti, Bayan Kyakkyawar Kulawar Da Suke Samu Ta Bangaren Abinci Tun Bayan Da Suka Dawo Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *