Wednesday, January 15
Shadow

Tinubu Ya Himmatu Wajen Rage Raɗaɗin Da ‘Yan Nijeriya Ke Ciki, Inji Minista

Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce Shugaba Bola Tinubu ya ƙudiri aniyar rage raɗaɗin da ‘yan Nijeriya ke ciki.

Idris ya bayyana haka ne a ranar Lahadi a Kaduna a shirin ‘Hannu Da Yawa’ na Gidan Rediyon Tarayyar Nijeriya (FRCN), Sashen Hausa.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa ministan ya yi magana kan wahalar da aka samu sakamakon cire tallafin man fetur, kuma ya ce tallafin yana amfanar wasu tsirarun mutane ne kawai.

Ya ba da tabbacin cewa tattalin arzikin ƙasar nan zai daidaita, kuma babu wata gwamnati da za ta so a samu ci-baya a zamanin ta.

Idris ya jaddada cewa abin da ya kamata a gyara a ƙasar nan ba ya ta’allaƙa ne ga Majalisar Dokoki ta Ƙasa, wakilai da aka zaɓa ko kuma masu zartaswa na gwamnati kawai ba ne, amma har ga duk ‘yan Nijeriya ne.

Karanta Wannan  Obaseki ya ce ba ya fargabar binciken EFCC

Ya yi nuni da cewa a kwanakin baya Tinubu ya umurci ministoci da su rage kuɗin gudanar da mulki ta hanyar taƙaita yawan motocin su a lokacin da suke gudanar da ayyukan su da kuma yawan ma’aikatan su a lokacin tafiye-tafiye.

Idris ya ce, “Shugaba Tinubu yana nuna buƙatar a sauya daga yadda ake tafiyar da al’amura a Nijeriya.

“A duk lokacin da muka zauna taron Majalisar Zartaswa ta Tarayya (FEC), abin da Shugaban Ƙasa ke jaddadawa shi ne buƙatar a rage kashe kuɗaɗe da yawa waɗanda ba su zama dole ba wajen gudanar da mulki.

“Shugaba Tinubu har ma ya ba da sanarwa kan kuɗin tafiya da yawan ababen hawa. Ana iya ganin wannan a matsayin abu ƙanƙani, amma a zahiri yana da muhimmanci.”

Ministan ya ce ta fuskar noma, Tinubu ya ce an canja wa Ma’aikatar Noma da Raya Karkara suna zuwa Ma’aikatar Noma Da Samar Da Abinci ta yadda za a magance matsalolin noma ta ɓangarori daban-daban.

Karanta Wannan  Gwamnan Jihar Kano Tare Da Sarki Sunusi ll Sun Gudanar Da Hawan Sallar Idi A Yau

Haka zalika ya bayyana cewa Tinubu na magance matsalolin rashin tsaro kai-tsaye, inda ya ƙara da cewa tun kafin zuwan gwamnatin sa ne ake fuskantar matsalolin.

Idris ya ƙara da cewa har yanzu Gwamnatin Tarayya tana kan hanyar samar da dandamali da kuma tabbatar da jin daɗin jami’an tsaro domin inganta tsarin tsaron ƙasa.

Ya ƙara da cewa har yanzu Shugaban Ƙasa na neman shawarwari kan ba samar da ‘yan sandan jihohi.

Da yake ƙarin bayani, Idris ya ce ɗauke wutar lantarki da aka yi a sassan arewacin ƙasar nan kwanan nan ba wani shiri ne aka yi ba kamar yadda wasu suke cewa.

Ya nanata cewa babu wani shugaba da zai so da gangan al’ummar sa su kasance cikin halin rashin wutar lantarki da sauran matsaloli.

Karanta Wannan  Kalli 'yan damfarar yanar gizo 24 da aka kama a Abakaliki

Ministan ya ƙara da cewa, “Shugaban Ƙasa yana bakin ƙoƙarin sa wajen ganin an samar da dauwamammiyar mafita kan matsalar lalacewar wuta a ƙasar nan.

“Haka nan ana gab da kammala aikin bututun iskar gas na AKK wanda zai taimaka wajen inganta masana’antu a Arewa.”

Idris ya buƙaci jama’a da su riƙa amfani da kafafen sadarwa na zamani wajen yaɗa labaran ƙasar nan ta hanyar da ta dace, yana kokawa da yadda ake yaɗa labaran ƙarya.

Ministan, yayin da ya yarda cewa lamari ne da ya shafi duniya, ya buƙaci yin amfani da kafafen ta hanya mai kyau.

Hoto:
Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai Alhaji Mohammed Idris (a tsakiya), tare da mai gabatar da shirin “Hannu da Yawa”, Malam Buhari Auwalu (a hahu), da Darakta-Janar na FRCN, Dakta Mohammed Bulama (a dama)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *