Friday, December 6
Shadow

Tinubu ya rantsar da sababbin ministoci

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya rantsar da sababbin ministocin da ya naɗa a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Da yake jawabi jim kaɗan bayan rantsar da su, Tinubu ya ce, “mun fara ƙoƙarin dawo da tattalin arzikinmu cikin hayyacinsa,” in ji shi, sannan ya ƙara da cewa, “muna kan tafarki mai kyau domin cika burinmu, ba ma don mu kaɗai ba, har da jin daɗin ƴaƴanmu da jikokinmu.”

Shugaban ƙasan ya ce duk da ƙalubalen da ake fuskanta, ana ci gaba da aikin inganta tattalin arzikin ƙasar.

Sai ya bayyana wa sababbin ministocin cewa an zaɓo su domin su bayar da gudunmuwarsu domin ceto ƙasar.

Karanta Wannan  Kalli Hoton Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, Atiku Abubakar da Peter Obi da ya dauki hankula

A ranar 23 ga Oktoba ce Tinubu na cire wasu ministoci guda biyar, sannan ya naɗa wasu guda bakwai.

A ranar 30 ga Oktoba kuma Majalisar Dattawa ta tantance tare da amincewa da sababbin ministocin wato: Ministan jinƙai da rage talauci Dr Nentawe Yilwatda da inistan ƙwadago, Muhammadu Maigari Dingyadi da ƙaramar ministar harkokin waje, Bianca Odumegwu-Ojukwu.

Sauran su ne; Ministan masana’antau da kasuwanci da zuba jari, Dr Jumoke Oduwole da ministan kula da dabbobi, Idi Mukhtar Maiha da ƙaramin minstan gidaje, Yusuf Abdullahi Ata da ƙaramar ministar ilimi, Dr Suwaiba Said Ahmad.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *