
Yayin da har yanzu gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu bata cika shekaru 2 da kafuwa ba, an fara yakin neman zaben 2027 dan ganin ya zarce.
Duk da yake shi shugaban kasar ko Jam’iyyar APC a hukumance basu bayyana fara yakin neman zaben ba.
Amma wasu jigo a Gwamnatin irin su shugaban Jam’iyyar APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje da Sakataren Gwamnati, George Akume sun bayyana neman Shugaba Tinubu ya zarce.
A yayin da yake ganawa da wasu ‘yan Jam’iyyar a hedikwatar Jam’iyyar dake Abuja, Ganduje yace ‘yan siyasa masu son tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2027 su dakata sai bayan 2031 idan Tinubu ya gama wa’adinsa na shekaru 8 akan mulki.
Hakanan shima Akume a wata hira da aka yi dashi a gidan talabijin na ChannelsTV yace yace Atiku Abubakar ya dakata da neman zama shugaban kasa a 2027.
Hakan an ga fastocin yakin neman zaben Tinubu a karo na 2 a jihohin Kebbi, Kaduna, Kwara da babban birnin tarayya, Abuja.
Tuni dai ‘yan Jam’iyyar Adawa suka fara Allah wadai da wannan mataki.
Hakan ya sabawa dokar kundin tsarin mulkin Najeriya.