Fitaccen Attajirin nan na duniya, Bill Gates wanda shi ne shugaban gidauniyar Bill da Melinda, ya ce harajin da ake karba a Nijeriya ya yi kadan.
Bill Gates ya yi bayanin hakan ne a taron tattaunawa na matasa kan samar da abinci mai gina jiki a Abuja a jiya Talata.
Majiyar mu ta Daily Nigerian Hausa daga Daily Trust ta rawaito cewa, Attajirin dan kasar Amurka yazo Nijeriya ne domin halartar taruka.
Da yake jawabi a taron, Bill Gates, ya ce karancin haraji da ake karba yana haifar da kalubalen kudi a fannin lafiya da ilimi.
Ya ce domin yan kasa su samu karfin gwiwa kan kokarin gwamnati na kula da lafiya dole ne a tabbata ana tafiyar da kudaden da ake warewa fannin lafiya a yadda ya dace.
Bill Gates ya ce, ” Tsawon lokaci akwai shirye shirye ga Nijeriya wajen samar da kudade ga gwamnati fiye da yadda ake a yanzu. Abinda Nijeriya ke karba na haraji ya matukar kadan”, inji shi.
Me zaku ce?