Saturday, August 15
Shadow

YANZU-YANZU: Rarara Ya Bada Kyautar Naira Miliyan Goma Ga Waɗanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Maiduguri

Rarara Ya Bada Kyautar Naira Miliyan Goma Ga Waɗanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Maiduguri

Mawaƙi Dauda Kahutu Rarara, ya bayar da gudunmuwar Naira miliyan 10 domin a tallafawa waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri.

A rahoton da Jaridar Dokin Ƙarfe TV ta samu, Rarara ya jajantawa Gwamna Babagana Zulum, Da mai martaba Shehun Barno a yayin ziyarar da Ya kai musu.

Sannan Rarara ya ƙara jajantawa al’ummar jihar, musamman waɗanda suka yi asara sakamakon ambaliyar ruwan.

A yayin ziyarar jajen, Rarara ya samu rakiyar Hajiya Aysha Humaira, Dak Abdullahi Al-Hikimah, Alan Waƙa, da Onarabul Auawal Ahmed Bakori da sauransu.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Matashiya 'yar Jihar Bauchi me shekaru 19 ta na neman mijin aure me Hankali, Mahaifinta me kudi ne amma tace ita matashi indai yana da sana'a da nutsuwa zasu daidaita

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *