
Daga Muhammad Kwairi Waziri
Fitaccen matashi Dudu Walle ya kama hanyar tafiya da ƙafa daga Adamawa zuwa Katsina domin nuna goyon bayansa ga mawaki Dauda Kahutu Rarara, da kuma halartar gaisuwar rashin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, a garin Daura.
A cewarsa, “Na yi bankwana da mutanen Adamawa, kuma idan an bani keke a hanya zan hau, amma idan babu zan ci gaba da tafiya da ƙafata.”
Al’umma da dama sun bayyana sha’awarsu da ƙarfafa masa gwiwa bisa irin wannan ƙudurinsa na nuna kauna da jajircewa.
Wane fata zaku masa?