
Shahararriyar Tauraruwar fina-finan kudu, Halima Abubakar ta bayyana a wani Bidiyo tana neman taimakon jama’a inda tace ta talauce.
Ta bayyana hakane a shafinta na Instagram inda tace itace da kanta ba karya ba.
Tace ta Talauce ta yanda yanzu haka ta sayar da motocin ta 3 inda ta koma kauyensu da zama.
Tace ta gaji da rokon mutane ‘yan uwa da abokan arziki kudi shine ta fito take son jama’a su taimaka mata inda ta ajiye account Number.
Tace an dakatar da ita daga harkar fim ta Nollywood dan haka yanzu bata da aikin yi.