Monday, March 24
Shadow

Akwai Tubabbun ‘yan Bìndìgà 789 da muke canjawa hali zamu kuma mayar dasu cikin al’umma su zauna>>Inji Sojoji

Shugaban sojojin Najariya, Gen. Christopher Musa ya bayyana cewa, akwai Tubabbun ‘yan Bindiga 789 da suke canjawa hali kuma zasu mayar dasu cikin mutane su zauna.

Musa ya bayyana hakane a wajan wani taron masu ruwa da tsaki da ya wakana ranar Talata a Abuja.

Yace An samu ‘yan Bindigar da yawa hakane saboda ‘yan Bòkò Hàràm da yawa da ake samu suna tuba.

Yace jimullar ‘yan Bòkò Hàràm 120,000 ne suka tuba suka mika wuya tun bayan da aka fito da tsarin karbar tubabbun ‘yan Bòkò Hàràm din dan canja musu hali.

Ya kara da cewa, yanzu haka akwai guda 789 da ake shirin yayewa daga shirin na canja musu hali dan su koma cikin jama’a da zama.

Karanta Wannan  Hotuna: Kwalliyar Sallah ta Tauraruwar me taimako kuma 'yar Kasuwa, Laila Usman da Mijinta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *