Wani gurin dake yin gwajin kwayoyin halitta na DNA dake legas me suna Smart DNA ya wallafa bayanan dake dauke da wanda suka fi yin gwajin a tsakanin kabilun Najeriya.
Shi dai gwajin DNA a mafi yawanci ana yinsa ne idan miji na zargin matarsa ta yi tarayya da wasu maza a waje ta kawo masa dan da ba nasa ba gida.
Dan haka idan wannan zargi ya shiga sai a je wajen gwaji a yi gwajin na DNA dan tabbatar da dan da ake takaddama akansa ko na mijin ne ko kuwa a’a.
A bayanan da Smart DNA suka fitar,sun ce kaso 53 cikin dari watau fiye da rabi, yarbawane ke zuwa yin wannan gwaji,sai kuma kaso 33.1 Inyamurai ne ke zuwa yin wannan gwaji, sai kuma kaso 1.20 Hausawa ne kezuwa yin wannan gwaji.
Bayanan sun bayyana cewa, 1/4 na mazan da sukw zuwa yin wannan gwajin ana gano cewa ba sune suka haifi ‘ya’yansu ba.
Hakanan rahoton ya nuna cewa, kaso me yawa na wanda ke yin wannan gwaji suna yi ne dan su fita zuwa kasashen waje.