Friday, December 5
Shadow

Zan tsaya takarar shugaban kasa a 2027, ba zan janyewa kowa ba>>Inji Rotimi Amaechi

Tsohon gwamnan jihar Rivers da ke kudu maso kudancin Najeriya, kuma jigo a jam’iyyar ADC, Rotimi Amaechi ya ce babu-gudu-ba-ja-da-baya a kan takarar shugaban kasa da yake son yi a 2027.

A wata hira da ya yi da manema labarai a Kano, Amaechi wanda kuma ya kasance ministan sufuri na kasar daga 2015 zuwa 2022, a lokacin gwamnatin Buhari, ya ce babu batun yin sulhu idan aka zo zaben fid da gwani a jam’iyyar ADC.

Ya tabbatar da cewa kowa yana da damar fitowa takarar shugaban kasa kamar yadda tsarin jam’iyyar ya nuna.

Amaechi ya bayyana haka ne yayin wani taro da hadaddiyar kungiyar ‘yan kasuwar jihar Kano da suka gayyace shi, inda ya ce abu ne mai kyau kowa ma ya fito takarar shugaban kasa a jam’iyyar ADC in ya so tasa ta fissheshi.

Tsohon gwamnan na Rivers, ya ce akwai kyakkyawar damar kawar da shugabancin Tinubu a zaben 2027, inda ya caccake shi musamman a kan salon yadda yake neman kuri’un ‘yan Najeriya.

Karanta Wannan  Gwamnatin Nijeriya Ta Yi Maraba Da Naɗin Maryam Bukar Hassan A Matsayin Jakadiyar Zaman Lafiya Ta Duniya

Ya ce : “Ko gwamnati tana son shirya zabe na gaskiya ko ba ta so, babu makawa sun gama yawo sai sun tafi saboda babu wanda ke jin dadin Tinubu ko a jihar Rivers har ma kudanci.

Kawai dai yana kokarin ya nuna zabe ne tsakanin ‘yan kudu da arewa, shi ya sa ‘yan kudu ke tambayarsa wadanne ‘yan kudu ne za su bi shi?

Saboda ko mukaman da yake bayarwa, ba ya bai wa ‘yan kudu. Ko Yarabawa ma ba ya ba su, kawai yana bai wa wasu mutane ne wadanda suka yi aiki da shi. Shi ya sa ba su damu da halin da jama’a suke ciki ba, sun fi damuwa da hadakar ‘yan mahayya.

Shi ya sa suke daukar nauyin wasu mutane su shiga kawancen don su haifar da rikici, suna ganin idan suka fito da kudi mutane za su tafi tare da su”.

Dangane da yadda manyan jam’iyyun kasar, APC da PDP suka bayyana cewa ‘yan takarar shugaban kasa na zaben 2027 za su fito ne daga kudancin Najeriya, ko su ma a jam’iyyarsu ta ADC, za su yi hakan sai ya ce shi bai sani ba.

Karanta Wannan  Majalisar Dattawan Najeriya ta kafa kwamitin kula da mulkin jihar Ribas

“Ni ban sani ba. Ni ba ADC ba ne. Ni mamba ne na jam’iyyar. ADC ce ke da alhakin tattaunawa ta ga ko akwai bukatar hakan sannan su yanke shawara. Ni mamba ne kawai. Duk shawarar da jam’iyyar ta tsayar zan yi na’am da hakan,” in ji shi.

‎‎‎Tsohon ministan na sufuri ya jaddada aniyarsa ta neman takarar shugaban kasar a 2027 a jam’iyyar ADC.

Ya ce: ”Zan shiga takara a zaben fid da gwani a ADC. Kuma ina addu’ar na yi nasara domin na fuskanci Tinubu.

‎A kan ko idan jam’iyyar ta nemi a yi maslaha a tsakanin ‘yan takara domin bar wa wani mutum daya, ko zai yarda ya bi, sai ya ce ai ba ma maganar janye wa wani.

”Ni takarar shugaban kasa zan yi. Ban ce zan janye wa wani ba. Zan tsaya takarar shugaban kasa, a bari jama’a su zabi wanda suke so ya zama shugaban kasa.

Karanta Wannan  Da Duminsa: An samu Matuka jirgin saman Air Peace da shaye-shayen abubuwan Maaye

”Idan ka duba duk masu neman takara a kasar nan, don Allah ka gaya mun wanda ya fi dacewa ciki har da Tinubu? Ni na fito daga kudu. Kudu ba sa rigima da kudu maso yamma. Ba ma rigima da kudu maso gabas. Sannan kuma ba ma rigima da arewa.” Ya ce.

Da dama dai na ganin tasirin Rotimi Ameachi a siyasance na disashewa musamman a jihar Rivers, saboda yadda tsohon gwamnan jihar kuma ministan Abuja a yanzu, Nysome Wike ke tayar da kura, amma a cewar Ameachi ba a nan gizo ke sakar ba.

Inda ya ce, ko a baya-bayan nan da ya ziyarci jihar don kaddamar da jam’iyyar ADC an ga yadda jihar ta yi cikar kwari da magoya bayansa tun daga filin jirgi ma, kuma a cewarsa babu wanda ya ba wa sisin kobo don a yi masa dafifi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *