Thursday, January 15
Shadow

Zanje in gana da Trump in warware masa zare da abawa>>Shagaba Tinubu bayan da Trump yayi bharhazanar kawo khari Najeriya

Fadar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta bayyana cewa nan gaba kadan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai gana da shugaban kasar Amurka, Donald Trump.

Me baiwa shugaban kasar shawara kan harkar sadarwa, Daniel Bwala ne ya bayyana hakan.

Yace a kwai kyakkyawar alaka tsakanin Najeriya da Amurka inda yace a baya Amurkar ta sayarwa Najeriya da makamai Wanda ta yi amfani dasu wajan yakar matsalar tsaro.

Hakan na zuwane kwana daya bayan da shugaban Amurkar, Donald Trump yayi barzanar kawo hari Najeriya idan gwamnati bata dauki mataki kan harkar tsaro ba.

Karanta Wannan  Manyan mutanen dake fitowa a matsayin malamai a fina-finan Hausa gara masu yin fina-finan Alfasha dasu>>Inji Dr. Hussain Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *