Monday, March 24
Shadow

Ƴansanda sun kama ƴan bìndìgà su na kokarin sayen ÀĶ-47 a Kano

Rundunar ‘Yansandan Jihar Kano ta kama wasu mutane hudu da ake zargi da zama ‘yan fashin daji waɗanda ake zargin suna kan hanyarsu ta sayen bindigar AK-47.

Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna, ya tabbatar da cafke waɗanda ake zargin a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar.

A cewarsa, rundunar ta samu gagarumar nasara a kokarinta na dakile yaduwar ‘yan fashin daji da miyagun laifuka a jihar.

Ya ce, “A ranar 6 ga Maris, 2025, da misalin karfe 2:00 na rana, wata tawagar jami’an bincike na ‘yansanda ƙarƙashin jagorancin SP Ahmad Abdullahi, jami’in da ke kula da ofishin ‘yansanda na Jar Kuka, sun cafke wasu mutane hudu da ake zargi da zama ‘yan bindiga a gidan man Chula dake Hotoro a Kano.

Karanta Wannan  Naga yanda kasar China take ta burgeni,Zan mayar da Najeriya kamar kasar China>>Shugaban Kasa, Bola Ahmad Tinubu

“Waɗanda aka kama sun haɗa da Shukurana Salihu, mai shekara 25; Rabi’u Dahiru, mai shekara 35; da Ya’u Idris, mai shekara 30, duk daga Jihar Katsina, da kuma Muktar Sani, mai shekara 30, daga Yandodo Hotoro , Kano. An kama su ne bisa sahihan bayanan sirri da suka nuna cewa sun zo Kano da niyyar sayen bindigar AK-47.”

Kiyawa ya de an samu wannan nasara ne sakamakon biyayya ga umarnin Sufeto-Janar na Ƴansanda, Kayode Adeolu Egbetokun, ga dukkanin rundunonin ƴansanda kan wani sabon salo na yaƙi da ta’addanci da laifuka a fadin ƙasar.

Ya kara da cewa an samu makamai, da harsashi da guru da layu da ƴaƴan boris da kuma kudi kimanin Naira Miliyan 1 da dubu 28 a tare da waɗanda ake zargin.

Karanta Wannan  Alamomin cikin wata tara

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *