
Wannan wasu ne daga cikin wadanda suka je wajan taron kaddamar da fara yiwa shugaba Tinubu ya kin neman zabe a jihar Kano.
Sunce sun kashe sama da dubu ukku kowannensu wajan hidimar zuwa wajan taron siyasar daga Aljihunsu.
Amma da aka tashi sallamarsu aka ba kowannensu dubu hudu, ko kudin motarsu da hidimar da suka yi ta zuwa wajan taron basu mayar ba.
Sunce indai tafiyar APC haka take, to ba zasu yi ba.