Saturday, May 17
Shadow

Na yi nadamar yiwa Tinubu yakin neman zabe, Jama’a ku yafe min kan jawo hankalinku da na yi kuka zabeshi>>Dan Balki Kwamanda

Dan siyasa a jiar Kano, Dan Balki Kwamanda ya bayyana nadama kan jawo hankalin mutane da yayi suka zabi shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a matsayin shugaban kasa.

Yace yayi nadamar yakin neman zaben da yawa Tinubu.

Yace tunda yake a rayuwarsa bai taba yin abinda yayi nadamarsa sosai ba kamar yiwa Tinubu yakin neman zabe.

Yace dalili kuwa shine alkawuran da Bola Ahmad Tinubu ya dauka be cika ba kuma mutane na cikin matsananciyar wahala.

Ya bayyana hakane a watan hira da gidan Jaridar Daily Trust suka yi dashi inda yace yana neman yafiyar wadanda ya yaudara.

Karanta Wannan  Manyan Arewa kudi aka basu suka siyar daku shiyasa suke gayawa shugaban kasa, Arewa ba korafi, Subul da baka ne aka yi a Katsina maganar ta fito fili amma dama can haka suke gayawa shugaban kasa, saboda an biyasu, Inji Sheikh Nura Khalid

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *