
Dan siyasa a jiar Kano, Dan Balki Kwamanda ya bayyana nadama kan jawo hankalin mutane da yayi suka zabi shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a matsayin shugaban kasa.
Yace yayi nadamar yakin neman zaben da yawa Tinubu.
Yace tunda yake a rayuwarsa bai taba yin abinda yayi nadamarsa sosai ba kamar yiwa Tinubu yakin neman zabe.
Yace dalili kuwa shine alkawuran da Bola Ahmad Tinubu ya dauka be cika ba kuma mutane na cikin matsananciyar wahala.
Ya bayyana hakane a watan hira da gidan Jaridar Daily Trust suka yi dashi inda yace yana neman yafiyar wadanda ya yaudara.