Saturday, December 13
Shadow

Nima Sanata Natasha Akpoti ta taba min sharrin wai naso yin lalata da ita amma na yi maganinta>>Inji Tsohon hadimin shugaban kasa, Reno Omokri

{“remix_data”:[],”remix_entry_point”:”challenges”,”source_tags”:[],”origin”:”unknown”,”total_draw_time”:0,”total_draw_actions”:0,”layers_used”:0,”brushes_used”:0,”photos_added”:0,”total_editor_actions”:{},”tools_used”:{},”is_sticker”:false,”edited_since_last_sticker_save”:false,”containsFTESticker”:false}

Tsohon hadimin shugaban kasa a zamanin mulkin tsohon ahugaban kasa, Goodluck Jonathan, Reno Omokri ya tabbatar da cewa, Sanata Natasha Akpoti ta taba masa kazafin cewa yana son yin lalata da ita.

Yace akwai wata kawar Sanata Natasha Akpoti wadda taso ya nemeta ya kiya.

Yace daga nan ne kawai sai ya ji Natasha Akpoti wadda a wancan karin ba sanata bace tace wai ya nemi yin lalata da ita a ranar da tsohon shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta ya kawo ziyara Na3.

Yace abin mamaki shine a wancan lokacin ba ya ma Najeriya, shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya aikashi ya wakilceshi a kasat Amurka kuma har ya dauki hotuna da wakilan kasar Amurka da yawa.

Karanta Wannan  Idan ku ka amince a ƙaro mana tankar yaƙi 50 to a wata biyu za mu gama da ƴan ta'adda - Ministan tsaro

Yace bayan da ya dawo ya hadu da zargin da Natasha ke masa, sai ya gabatar da hujjojinsa wanda da taga ba zata yi nasara ba, sai ta goge duka zarge-zargen da take masa a kafafen sada zumunta.

Yace saidai a yayin da yake tunanin matakin da zai dauka akanta, sai wani babban mutum da yake ganin girmansa ya kirashi ya bashi baki inda aka sasantasu.

Yace abinda ya faru tsakaninsa da Sanata Natasha Akpoti kenan amma bai san komai ba game da zargin da takewa Sanata Godswill Akpabio ba saboda baya wajan.

Yace kafafen watsa labarai da yawa nata kiransa dan yayi hira dasu akan lamarin amma gashinan abinda ya sani kenan game da sanata Natasha Akpoti.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Yanda Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya budewa mataimakin shugaban kasar Brazil kofa, sai sukarsa ake na cewa ya zubarwa da kansa Daraja

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *