
Wannan Bidiyon ya nuna yanda aka kai Amarya, Tauraruwar fina-finan Hausa, Maryam Malika gidan mijinta, kuma abokin aikinta, Abdul M. Shareef.
An ganta tana zubar da hawaye, kawaye na mata tsiya.
Saidai wasu sun yi mamakin yanda take kukan Amarci ganin cewa, Bazawarace.
Malika dai ta yi aure na farko inda ta fito ta ci gaba da fim amma yanzu Allah ya azurtata da sake yin wani auren.
Muna wa ma’auratan fatan Alheri.