Babban Limamin Masallatan Harami Sheikh Abdurrahman Sudais ya sanar cewa za a fassara hudubar Ranar Arafa kai-tsaye a cikin harshen Hausa da wasu harsuna 19 domin karuwar alhazai da sauran al’ummar Musulmi a fadin duniya.
Sheikh Sudais ya ce ana sa ran sama mutum miliyan 100 za su saurari hudubar wadda Sheikh Maher Al Mu’ayqaly zai gabatar a Masallacin Namirah ta kafofin watsa labarai daban-daban.