Saturday, June 27
Shadow

Shugaban FRSC ya koka kan rashin ɗa’a da cin hanci a tsakanin jami’an hukumar

Shugaban FRSC ya koka kan rashin ɗa’a da cin hanci a tsakanin jami’an hukumar.

Shugaban Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC), Shehu Mohammed, ya bayyana damuwa kan ƙaruwar rashin ɗa’a da cin hanci da shan miyagun ƙwayoyi daga wasu jami’an hukumar, yana mai gargadin cewa hakan na iya lalata amincewar jama’a da mutuncin hukumar.

A yayin taron tsakiyar shekara da aka gudanar a Abuja, Mohammed ya umurci manyan jami’ai da su dauki matakai kan wadannan kalubale tare da tabbatar da ladabtarwa da gaskiya a tsakanin ma’aikata. Ya ce hukumar za ta ladabtar da wadanda suka sabawa ka’idoji tare da yabawa masu bin doka domin karfafa gwiwa.

Karanta Wannan  Da Duminsa: Tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya bayyana matsayarsa game da tsayawa takara a 2027

Shugaban FRSC ya bayyana cewa gwamnati ta amince da gyaran dokar hukumar da zai sauya sunanta zuwa Nigeria Road Safety Commission, tare da fadada aikinta zuwa dukkan titunan jama’a da kafa rundunar musamman.

Duk da kalubalen ciki, Najeriya ta samu lambar yabo ta Kofi Annan Road Safety Award a matsayin kasa mafi kyau a harkar kiyaye hadurra a Afrika. Hakanan hukumar ta kara daukar matakan wayar da kan jama’a da amfani da fasahar zamani domin inganta ayyukanta.

Mohammed ya yi kira da karin hadin kai tsakanin jami’an hukumar da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da ingantaccen aiki da rage hadurran mota a fadin kasar.

Karanta Wannan  Kalli Hotuna da Bidiyo yanda Ake zargin dan shugaban kasa, Seyi Tinubu yawa shugaban daliban Najeriya Tsirara yasa aka masa dukan kawo wuka jikinsa Duk burdi, kawai dan yace ba zai karbi Naira Miliyan 100 ba ya goyi bayan Tinubu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *