
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya sake bayar da umarnin a sake rage farashin kayan abinci.
Shugaban ya bayar da wannan umarnin ne ga majalisar zartaswa, kamar yanda karamin Ministan noma, Senator Aliyu Sabi Abdullahi ya bayyanawa manema labarai a Abuja.
Ministan da yake magana ranar Laraba ya ce shugaban kasar yace a samar da yanda za’a rika safarar kayan abincin a Najeriya ta hanyar sauki ta yanda farashinsa zai sake sauka.
Hakan na zuwane a yayin da wasu manoma ke kukan cewa faduwar farashin kayan abinci na sa su tafka Asara.