Thursday, February 5
Shadow

Babu Yunwa a Najeriya>>Inji Me magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga

Me magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya musanta ikirarin tsohon Mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar cewa akwai yunwa a Najeriya.

Atiku yace yunwar dake Najeriya da Talauci ka iya tunzura mutane su fita zanga-zanga irin wadda ake yi a kasashen Duniya.

Saidai me magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya musanta maganar ta Atiku inda yace Atiku be san halin da Najeriya take ciki ba a yanzu dan an kama hanyar ci gaba.

Yace Hukumar kididdiga ta kasa, NBS ta fitar da bayanai cewa farashin kayan masarufi sun yi kasa, sannan a baya tace kudaden shigar Najeriya sun karu ta bangaren da ba na man fetur ba.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon katafaren masallacin da Dauda Kahutu Rarara ya gina a mahaifarsa dake Kahutu

Sannan yace Tinubu ya biya basuka da yawa da ake bin Najeriya.

Yace kuma Tinubu ya dauki matakai na gyara kasa ba tare da tsoro ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *