Thursday, February 5
Shadow

A bayyana mana sunayen Maqiya Dimokradiyya da suka so yiwa Gwamnatin Tinubu juhyin Mulki>>Mahdi Shehu ya roki Gwamnatin Tarayya

Dan Gwagwarmaya, Mahdi Shehu ya bayyana cewa, ‘yan Najeriya suna nema kuma suna da ‘yancin a sanar dasu sunayen sojojin da suka shirya yiwa Gwamnatin Tinubu juyin Mulki.

Ya bayyana hakane a shafinsa na X inda yace sati uku kenan ana ta rade-radin cewa an yi yunkurin yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu juyin Mulki.

Yace magana dai tun ana jita-jita har ta zama gaskiya inda yace ya kamata a daina boye-boye a fito a gayawa ‘yan Najeriya su waye suka shirya wannan juyin Mulki?

Karanta Wannan  Sowore ya baiwa 'yan Najeriya shawarar su je su shiga gidaje 753 na Abuja da gwamnati ta kwace saboda nasu ne

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *