Wednesday, May 6
Shadow

Me ya Faru? Malam Nasiru Ahmad El-Rufai zai ci gaba da zama a hannun ICPC duk da kotu ta bayar da belinsa

Rahotanni sun bayyana cewa, tsohon Gwamnan kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai zai ci gaba da zama a hannun hukumar ICPC duk da cewa kotu ta bayar da belinsa.

Mai shari’a na babbar kotun tarayya dake Kaduna, Justice Rilwanu Aikawa ne ya bayar da belin malam Nasiru Ahmad El-Rufai a ranar Talata.

Bayan bayar da belin nasa, El-Rufai yaki yin magana da manema labarai amma wani na kusa dashi ya shaidawa jaridar Daily Trust cewa, kotu ta saka sharuda 10 akan belin na Malam Nasiru Ahmad El-Rufai.

Yace sai an cika wadannan sharudanne sannan za’a sakeshi.

Karanta Wannan  'Yan Arewa bayin Allah ruwa Kwata suke sha, sai da Peter Obi ya tausaya ya je ya gina musu fanfon burtsatse sannan suke samun ruwan sha me kyau>>Inji Wannan masoyiyar Peter Obin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *