
Sanata Shehu Sani daga jihar Kaduna ya bayyana cewa shekarun sa ba su kai ba, yayi kankanta sosai ace an nadashi jadakan Najeriya zuwa wata kasa.
Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi inda aka tambayeshi game da rahotan dake cewa shugaba Tinubu ya bayar da sunansa cikin wanda zai baiwa mukamin Jakadanci.
Sanata Shehu Sani yace har yanzu yana da ayyukan da zai wa Al’ummarsa a Kaduna Tukuna.