Tuesday, January 20
Shadow

Kalli Bidiyon ganawar da shugaba Tinubu yayi da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya gana da Gwamnan kano, Abba Kabir Yusuf a fadarsa dake Abuja a yammacin ranar Litinin.

Ganawar tasu na zuwane yayin da ake ta rade-radin cewa, Gwamna Abba Kabir Yusuf zai koma jam’iyyar APC.

A sanarwar da me magana da yawun gwamnan, Sunusi Dawakin Tofa ya fitar, yace gwamna Abba ya gabatarwa da shugaba Tinubu tsare-tsaren gwamnatinsa ne da suka hada da samar da Tsaro, da Ayyukan ci gaba da kuma Hada kai da Gwamnatin tarayya.

A sanarwar da Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas ya fitar, yace a yau, Talata ne Gwamna Abba Kabir Yusuf zai karbi katinsa na zama dan jam’iyyar APC.

Karanta Wannan  Ba wai Lusarin Mataimakin Gwamnan da bashi da katabus a jihar Bauchi ba, wallahi ko Gwamnan Bauchi ya sake ya mari babana da sai Babana ya faffasa mai baki da hanci>>Inji Dan Ministan Harkokin kasashen waje, Yusuf Tuggar inda yace karyane ba'a mari babansa ba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *