
Wasu matasan Sojojin Najeriya na ci gaba da shan ruwan Allah wadai bayan da suka shiga gasar rawa a Tiktok.
Gasar rawar ta samo asali ne bayan da wata matashiya ta bayyana ta soke waya a kugunta tana rawa, Bidiyon ta ya watsu sosai inda akai ta kwaikwayarta.
Suma matasan sojojin sanye da kakinsu, an gansu sun yi irin wannan rawa sun dora a shafinsu na sada zumunta.
Saidai lamarin ya jawo musu Allah wadai.