Friday, May 1
Shadow

Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya ce har yanzu yaki Amsa k9 daya daga cikin Tambayoyin da ICPC suke masa

Tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa, har yanzu bai amsa tambaya ko daya ba cikin Tambayoyin da ICPC suke masa.

Malam Nasiru Ahmad El-Rufai dai ya shafe kusan sama da sati biyu kenan a hannun ICPC tun da suka karbeshi daga hannun EFCC.

Ya bayyana cewa, dalilin da yasa ya ki amsa tambayoyin nasu shine binciken da ake masa na da alaka sa diyasa.

A baya dai ICPC ta kai samame gidan Malam Nasiru Ahmad El-Rufai inda tace ta gano abubuwa da yawa ciki hadda wata na’ura ta yiwa waya kutse.

A baya dai malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya yi ikirarin yiwa wayar me baiwa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro, Malam Nuhu Ribadu kutse.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Malam Aminu Ibrahim Daurawa ya jaddada Fatawarsa ta cewa akwai inda aka yadda mace ta yi shugabanci duk da Sùkàr da ake masa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *