Monday, March 23
Shadow

Kayan Masarufi zasu yi tsafmda kuma Talauci zai karu, Inji Shugaba Tinubu

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya yi gargadin cewa rikicin gabas ta tsakiya zai iya shafar Najeriya ta hanyar da kayan masarufi zasu yi tsada sannan karancin kudi a hannun mutane zai yi kamari.

Shugaban ya bayyana hakane a Legas yayin da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da wasu gwamnoni 23 suka je masa gaisuwar Sallah.

Shugaban yace zuwansa Ingila abinda suka fi baiwa muhimmanci shine hadaka da samarwa Najeriya kayan aiki dan magance matsalar tsaro.

Shugaba Tinubu yace ya kuma yi magana da shugaban kasar Faransa shima yayi alkawarin baiwa Najeriya kayan aiki dan magance matsalar a tsaro.

Yace kuma yana nan yana kara tuntubar sauran wasu shuwagabannin.

Karanta Wannan  Duk sojan da aka kama ya na shan Wiwi ko ƙwaya zai ɗanɗana kuɗar da>>Kwamanda

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *