
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya yi zargin cewa, Gwamnati na son kama yayansa, Bashir El-Rufai dan a tursasashi ya amince da bukatun Gwamnatin.
Yace dalili ma kenan da yasa suka ce babban yayan nasu ya tsaya a birnin Cairo na kasar Egypt kada ya dawo Najeriya dan kar a kamashi.
Yace yanzu haka yana can.
ElRufai ya bayyana hakane a wajan zaman makokin mahaifiyar sa data rasu inda yakewa mutane godiya da irin aoyayyar da suka nuna musu.