
Ministan tsaro, Christopher Musa ya baiwa sojojin Najeriya umarnin kada su sake sauraren umarni, duk inda suka ga dan Bìndìgà su aikashi kiyama.
Ya bayyana hakane a yayin ziyarar da ya kai rundunar operations hadin kai dake Maiduguri.
Ko sa a baya lokacin yana shugaban sojojin Najeriya, Christopher Musa ya taba bayar da irin wannan umarni wanda ya jawo masa yabo sosai.