
Mawallafin jaridar Sahara Reporters kuma me ikirarin fafutukar kare hakkin bil’adama, Omoyele Sowore ya bayyana cewa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ne ya dauki nauyin me son kafa kasar Yarbawa ta Oduduwa watau Sunday Igboho dan ya kawo matsala a gwamnatin Buhari.
A wancan lokacin dai, lamari yayi kamari har sai da ta kai ga Sunday Igboho ya tsere daga Najeriya dan gujewa kamun hukumomi.
Saidai a yanzu ya dawi gida Najeriya har ma ana damawa dashi a Gwamnatin Tinubu.
Sowore ya bayyana hakane a wani shirin Podcast me suna Times a yayin da yake sharhi akan siyasar yankin yarbawa na Kudu maso yamma.
Yace a kokarin Tinubu na samun mulki shine ya fitar da kudi aka kafa kungiyar ta son ballewa daga Najeriya a kafa kasar Yarbawa ta Oduduwa.
Yace kuma Tinubu yayi hakane saboda a wancan lokacin suna da matsala da Buhari inda ake tattauna cewa ba za’a amince dashi a matsayin dan takarar jam’iyyar APC ba.