
Rahotanni daga jihar Jigawa na cewa, Gwamnan jihar ya kulle asusun kananan hukumomin jihar har na tsawon watanni 3 bayan da ya gano suna Almubazzaranci da dukiyar al’umma.
Gwamnan ya dauki wannan matakinne bayan gano cewa wasu daga cikin shuwagabannin kananan hukumomin na ware Naira Miliyan 70 dan yin Adashi.