Sunday, April 12
Shadow

Da Duminsa: Ganduje da Doguwa sun bayyana wanda suke son a baiwa mataimakin gwamnan jihar Kano

Dan majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa da Tsohon shugaban jam’iyyar APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje sun bayyana wanda suke so a baiwa Mataimakin Gwamnan jihar Kano.

Duka su biyun sun bayyana Murtala Garo a matsayin wanda suke son a baiwa mataimakin Gwamnan jihar ta Kano.

Doguwa ya bayyana hakane a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja.

Rahoton yace an cimma matsayar a zabi garo a matsayin mataimakin Gwamnan jihar Kano ne bayan wani zama da masu fada aji na jam’iyyar APC a jihar Kano suka yi ranar Asabar.

Kuma kaso 90 cikin 100 na mutanen suka ce sun amince a zabi Garo a matsayin mataimakin gwamnan jihar.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Duk da cewar da ta yi ba zata yi ba, kalli yanda aka tursasawa Maryam Labarina yin wanke-wanke

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *