Saturday, August 15
Shadow

Da Duminsa: Ji matakin da Wike ya dauka dan hana ADC gudanar da babban taronta na yau

Jam’iyyar ADC ta sanar da samun wajen taro me zaman kansa na Rainbow a Abuja inda tace a canne zata gudanar da taron nata.

Hakan na zuwane bayan da jam’iyyar tace ta yi iya bakin kokarinta wajan karbar Eagles Square da Filin wasa na Moshood Abiola amma aka hanata.

Saidai wasu rahotanni dake fitowa sun ce Ministan Abuja, Nyesom Wike ya yi shirin aika jami’an tsaro dan hana taron na ADC a wajan taron na Rainbow.

Saidai jami’an tsaron sun gayawa Wike cewa, hakan ba zata yiyu ba saboda ‘yan Adawar na da yawa sosai kuma sun hada kawunansu da kyau.

Wike dai yace ADC karya take bata nemi wajan taron ba a hukumance yayin da ADC din kuma tace ta nema amma hanata aka yi.

Karanta Wannan  Dalilin da yasa Tinubu yaki baka Minista shine ka taba zagin Annabi Isa(AS), sannan An zarge ka da hannu a kkàshe 'yan Shi'a, sannan kuma ka yi barazanar kkàshè Turawa>>Reno Omokri ya mayarwa da El-Rufai Martani

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *