
Jam’iyyar ADC ta bayyana cewa wajan taro na Rainbow data shirya yin taronta na kasa a yau, Talata ya sanar da ita cewa ya fasa bata wajan.
Me magana da yawun ADC, Bolaji Abdullahi ne ya bayyana haka a wata sanarwa inda yace, Rainbow ya basu dalilin cewa, Hukumar kula da babban birnin tarayya, Abuja, FCTA ce ta musu barazanar cewa idan suka bayar da wajan za’a kwace lasisinsu.
Saidai Bolaji Abdullahi yace sun riga sun sakawa takardar yarjejeniya da raibow hannu dan haka ba zasu fasa ba a wajan zasu yi taronsu.