Wednesday, April 15
Shadow

Kalli Bidiyon yanda mutanen jihar Kwara suka ki karbar Tallafin shugaba Tinubu, Sun ce ba shine matsalarsu ba

Mutanen jihar Kwara sun ki karbar tallafin da aka kai musu na gwamnatin tarayya, karkashin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.

A wani Bidiyo da ya rika yawo a kafafen sada zumunta, an ga mutanen na jihar Kwara na cewa basa son tallafin kowa yaki karba.

Jihar Kwara dai na daga cikin jihohin dake fama da matsalar tsaro sosai.

A baya ma, Jihar Benue sun fito sun ce basa son tallafin shinkafa na Gwamnatin Tinubu inda suka ce ba shine matsalarsu ba.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon yanda wani dan Najeriya ya koma Kango da zama bayan da kudadensa da ya zuba a harkar Forex suka lalace

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *